News

Ana Zargin Jarumin Kannywood Sadik Sani Sadik Da Almundahana

Ana Zargin Jarumin Kannywood Sadik Sani Sadik Da Almundahana

Ana Zargin Jarumin Kannywood Sadik Sani Sadik Da Almundahana, A Yanzu Haka Kotu Na Nemansa Ruwa A Janlo.

A yau din nan majiyarmu hausaloaded ta samu wani rahoto wata kotu a jahar kano ta bada umurnin kamo fitaccen jarumi sadiq sani SadiQ ruwa jalo inda freedom radio na ruwaito cewa.

Wata Kotu a nan Kano ta Umarci ɗan Sandan Kotu daya kamo Mata jarumin wasan kwaikwayon nan Sadik Sani Sadik.

Kotun shari’ar musulunci da ke Zamanta a Hotoro masallaci ƙarƙashin mai shari’a Sagir Adamu ce ta bada umarnin kamo Sadik ɗin sakamakon bijirewa umarnin ta.

Tunda fari dai wani mashiryin Film ne wato Aliyu Adamu Hanas yai ƙarar sa sakamakon bashi kafin alƙalamin kuɗin aiki shirin wasan kwaikwayo shi kuma bai yi aikin ba kuma ake zargin ya hana shi kudin hakan yasa ya garzaya kotun domin roƙon ta nemar masa haƙƙin sa.

Kotun dai ta aike da sammaci amma ba a same shi ba ta kuma bada umarnin a liƙe masa takardar a gidansa da ke Tudun Yola amma har yanzu bai bayyana ba.

Wakilin Freedom Radio Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito cewar me ƙara yana neman Naira dubu tamanin a hannun Sadik ɗin kuma zai sake shigar da ƙara ta neman haƙƙin sa na ɓata masa lokaci da kuma jawo masa asara sakamakon rashin halartar aikin da yayi.”

Via. HAUSALOADED

360hausa Team

360Hausa is a current Best Hausa Entertainment blog in Africa that specialized in providing you high quality content. 360Hausa was found and manage by Abubakar Yusuf Radda (B2 [D Promoter] Slayer). A Blogger, Ghost Writer & Content creator. Follow us on Social Media @360Hausa

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button