Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Mayar Da Martani Kan masu sukarta.
A kan batun jaruma Nafisat Abdullahi kuwa, jama’a sun yi caa a kanta bayan ta caccaki iyaye masu haifar ‘ya’yan da basu iya kula da su ko suke tura su almajiranci. Jarumar da alamu abun ya yi mata zafi inda ta zage tare da mayar musu da martani bayan ganin abun ya yi yawa yadda ake ta batun ta a kafafen sada zumunta har da jaridu.
- Jaruma Nafisat Abdullahi ta yi martani ga masu zaginta kan batun haihuwar yaran da ba a iya kula da su ko ake tura su almajiranci
- Jarumar tace ta san ance a yi aure a hayayyafa, amma babu inda aka ce a haifa a watsar da su a titi babu kulawa
- Ta ce ga masu cewa ta bari tayi aure kafin ta saka baki a wannan harkar, ta ina wannan ya shafi aurenta? Ko cewa tayi ba za ta taba aure ba babu abinda za a iya a kai
Duk Wanda ya ji haushi na ce stop giving birth to kids you can’t cater for is definitely part of the problems our dear north/country is facing!!! And the least you can do is insult or say ‘go and get married’ that’s it!!! Allah ya Kyauta.
— Nafisat Abdullahi (@NafisatOfficial) April 17, 2022