Matan Kannywood Masu Yara 2022

Matan Kannywood Masu Yara 2022

Jerin Duk Matan Kannywood Masu Yara 2022.

A Baya Mun Kawo Muku ” Manyan Matan Kannywood 10 Masu Kudi“, Domin Kara Muku Ilimi Akan Masana’antar Film Ta Kannywood.

Wadannan Jerin Matayen Kannywood Ne Da Suke Da Yara, Wasu Daga Cikinsu Sunada Aure
Yayin Da Wasu Kuwa Sun Rabu Da Mazajen Nasu, Ga Cikakken Bayanin Nasu:

MATAYEN KANNYWOOD MASU YARA

1. Jamila Nagudu
Jaruma Jamila Nagudu Wacce Ta Jima A Masana’antar Ta Kannywood Tana Da Yaro Namiji
Guda Daya.
2. Rukayya Dawayya
Itama Jarumar Tana Da Yaro Guda Daya, Rukayya Dawayyah Ta Fara Harkar Kannywood Tun
Tana Budurwa Daga Baya Tayi Aure, Bayan Ta Samu Haihuwa Kuma Auren Nata Ya Mutu Ta
Dawo Kannywood.
3. Mansurah Isah
Tsohuwar Jarumar Kannywood Ce, An Haifeta A Kano Kuma Ta Tashi A Cikin Kano, Jaruma
Mansura Isah Yoruba Ce Wacce Ta Auri Abokin Aikinta Wato Sani Danja, Jarumar Tana Da
Yara Hudu A Yanzu, Maza Uku, Mace Daya.
4. Hadiza Gabon
Jarumar Ta Shigo Harkar Kannywood Da Yarta Guda Daya, Wanda A Yanzu Tana Nan Bata Da
Aure.
5. Samira Ahmad
Jarumar Kannywood Ce Wadda Ta Jima Tana Cikin Harkan Kannywood Din, I tama Ta Auri
Abokin Aikinta Wato Jarumi Tanimu Wanda Akafi Saninsa Da TY Shaba Daga Baya Suka Rabu,
Sun Samu Yarinya Daya, Yanzu Jarumar Tana Da Yarinya Daya Kuma Bata Da Aure.
6. Fati Muhammad
Fati Muhammad Tsohuwar Jarumace Da Ta Shiga Kannywood Tun Yana Sabo, Yar Fulani Ce
Wadda I tama Ta Auri Abokin Aikin Nata Wato Sani Mai I ska, Bayan Sun Samu Yara Biyu Mace
Daya Miji Daya Sai Daga Baya Auren Ya Mutu, Yanzu Tana Zaune Bata Da Aure.
7. Maryam Hiyana
Tsohuwar Jaruma Maryam Hiyana Wanda Tauraronta Ya Haska Tun Shekarar 2005, Ta Shiga
Kannywood Tun Tana Budurwa, Daga Baya Tayi Aure, Yanzu Tana Da Yara Kuma Tana Gidan
Mijinta.
8. Momee Gombe
Jaruma Momee Gombe Tayi Aure Sau Biyu, Kuma Tana Da Yara Biyu.
9. Hafsat Idris
Fitacciyar Jaruman Kannywood Wadda Akafi Sani Da Barauniya, Tayi Zafafan Fina-Finai Sama
Da 20, Jarumar Tayi Tana Da Yara Uku Namiji Daya Da Kuma Mata Biyu.
10. Aisha Najamu Izzar SO
Jaruma Aisha Najamu Wanda Tauraronta Ya Haska Sakamakon Shirn Izzar So, Ta Tabayin
Aure Amma Yanzu Auren Nata Ya Mutu Kuma Tana Da Yara Maza Guda Biyu.

Akwai Matan Kannywood Masu Yara Da Yawa, Ma’aikatan 360Hausa Na Bincike Don Gano Sababbi.

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Ad Blocker Detected

Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by disabling your ad blocker.

Refresh