HAUSA NEWS

Ya Kamata A Fara Yi Wa Duk Mai Mace Daya Bulala Har Sai Ya Kara Aure – Inji Malam Bello Yabo

Ya Kamata A Fara Yi Wa Duk Mai Mace Daya Bulala Har Sai Ya Kara Aure - Inji Malam Bello Yabo

Babban Malami Bello Yabo Yace Ya Kamata A Fara Yi Wa Duk Mai Mace Daya Bulala Har Sai Ya Kara Aure.

Aminiya ta labarto cewa; Malam Bello Yabo ya shawarci Gwamnatin Nijeriya da ta fito da wata doka da za a rika yi wa duk magidancin da ya shekara 10 da mata guda bulala 10 duk mako har sai ranar da ya kara aure.

 

Babban Malamin addinin musuluncin da ke Jihar Sakkwato, Sheikh Bello Yabo, ya yi kira ga gwamnatin da ta fito da dokar a wani bidiyonsa da a yanzu ya karade dandalan sada zumunta musamman a Facebook.

 

Malamin ya bayyana cewa ya taba karantawa cewar a wata kasa ana zane duk wanda ya kai wasu shekaru da mata daya har sai ya kara wata matar.

Hakan ce ta sanya malamin ya yi kira da Gwamnati da ta kirkiri wannan dokar a Najeriya ta zane duk wani mai mata daya har sai lokacin da ya kara aure.

 

Har ila yau, Malamin ya bayyana cewa mene ne amfanin namiji ya auri mata guda, inda kuma a cikin raha ya yi kira ga ‘yan Najeriya a kan kada su sake zaben duk wani dan siyasa mai mata daya.

Sai dai wannan lamari ya jawo tafka muhawara a shafukan sada zumunta inda mutane ke tofa albarkacin bakinsu a kan jawabin malamin, inda wasu take suka yi wa malamin raddi wasu kuma suka nuna goyon bayansu a kai.

 

Suleiman Baba Umar ya ce “ana maganar tsadar gero da masara da rashin kudi, amma maganar kara mata ita ce ta damu malamin”

 

Sai dai wasu kuma masu goyon bayan malamin sun bayyana cewa “bikin Magaji ba ya hana na magajiya” kamar yadda Abdulhamid Yahuza ya mayar wa Suleiman martani kan sukar da ya yi wa Malamin.

Wasu kuma ba su mayarwa da malamin wani martani ba, sai dai sun yi kira ga gwamnatin akan cewa bayan sanya dokar kuma ta kirkiri wata dokar ta bai wa su magidanta wani kudi na musamman domin cefanen yau da kullum.

 

360hausa Team

360Hausa is a current Best Hausa Entertainment blog in Africa that specialized in providing you high quality content. 360Hausa was found and manage by Abubakar Yusuf Radda (B2 [D Promoter] Slayer). A Blogger, Ghost Writer & Content creator. Follow us on Social Media @360Hausa

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button