Lectures

Yadda Zaka Janyo Hankalin Mace Ta Fara SONKA

Yadda Zaka Janyo Hankalin Mace Ta Fara SONKA

Ga Yadda Zaka Janyo Hankalin Mace Ta Fara SONKA.

Ka Taba Ganin Mace Wadda Ta Kwanta Maka A Rai Amma Da Kaje Mata Da Zancen Soyayya Sai Tace Maka Bata Yinka?

Ko Kuwa Kana Tunanin Koda Ka Fada Mata Zata Iya Kin Yarda Da Kai? Indai Kana Fargabar Wannan Yau Munzo Maka Da Mafita Insha Allahiu, Kamar Yadda Kowa Ya Sani Allah Ya Halicci Namiji Da Mace, Kuma Ya Sanya Soyayya A Cikinsu, Ta Yadda Zasu Iya Rayuwa Batare Da Kyamata Ko Makamancin Hakan Ba, Kana Iya Kamuwa Da Ciwon Mutum Koda Ace Bakayi Niya Ba, Kuma Soyayyar Mutum Yana Iya Shiga Zuciyarka Batare Da Ka Shirya Ba, Soyayya Yakan Iya Badda Kamanni Yazo Maka Ta Sifar Da Bakayi Tsammani Ba, Zaka Iya Kamuwa Da Ciwon Son Mutum Amma Abun Bakin Ciki Saika Samu Shi Baya Yinka Kwata-Kwata, Idan Kabi Wadannan Hanyoyi Insha Allahu Zaka Dace:

Da Farkon Farawa Ka Sanya Allah Ubangiji A Cikin Ranka, (Kayita Addu’a Akan Allah Ya Baka Mafi Alheri A Rayuwarka Tare Da Neman Tsari Daga Shaidan Dama Duk Wani Abinda Yake Mara Kyau A Gareka), Sa’annan Ka Yawaita Nuna Damuwa Akanta, Idan Kana Da Lambarta Ka Yawaita Kiranta Kuna Gaisawa Sa’annan Kan Nuna Mata Cewa Kana Kaunarta Tare Dayi Mata Dadadan Kalamai
Wadda Zasusa Hankalinta Ya Kwanta, Idan Kuma Bata Tsayawa Ta Saurari Wayarka Kaidai Kaci Gaba Da Kiranta. Sa’annan Ka Ringa Yi Mata Alheri, Idan Tana Da Yan Uwa Suma Ka Ringa Yi Musu Alheri, (Idan Har Baka Yiwa Mace Kyauta Babu Yadda Za’ayi Ta Soka) Don Haka Alheri Shine Babban Abinda Zaka Saka A Gaba.
Abu Na Karshe, Duk Lokacin Da Kuka Hadu Ka Saki Fuskarka Kayita Sanyata Dariya, Wasu Matan Basu Tsayawa Su Saurari Kalamai, Amma Idan Kanayi Mata Raha Kana Sanyata Nishadi Magana Ta Kare. Wadannan Sune Manyan Hanyoyin Da Namiji Zaibi Ya Janyo Hankalin Mace Ta Far Sonshi Batare Da Yana Kashe Kansa Da Cutar Zuciya Ba, Idanma Taki Ka To Ka Sani Saboda Addu’ar Da Kakeyi Allah Zai Taimakeka.

360hausa Team

360Hausa is a current Best Hausa Entertainment blog in Africa that specialized in providing you high quality content. 360Hausa was found and manage by Abubakar Yusuf Radda (B2 [D Promoter] Slayer). A Blogger, Ghost Writer & Content creator. Follow us on Social Media @360Hausa

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Related Articles

Back to top button