STORIES

Yadda Zaka Tunkari Budurwa Da Maganar Soyayya Ka Sace Zuciyarta Ta Sauki

maganar 360Hausa
Yadda Zaka Tunkari Budurwa Da Maganar Soyayya Ka Sace Zuciyarta Ta Sauki

Ina Masu Neman Ilimi Akan Soyayya ? To Ga Yadda Zaka Tunkari Budurwa Da Maganar Soyayya Ka Sace Zuciyarta Ta Sauki.

RANAR FARKON HADUWA.

Dazaran kaga macen da kakeso ko kuma ka dade kana sonta amma karasa yadda zakayi to kada kayi kasa a guiwa kawai kabi wadannan matakan insha Allah zakai nasara. Kada ka tsaida ita inda taron mutane yake domin bazata baka damar yin magana da ita ba, ka kasance mai tsabta sannan ka koyi dressing kafin ka tunkareka hakan zaisa ka burgeta ta samu kwarin gwiwar amsar soyayyarka. Idan kasamu damar gani fitowarta zataje wani wuri sai kabita sannu sannu a baya ammafa ka gyara takunka yadda ko juyowa tayi bazata gane cewa ita kakebi ba, idan kaga ankai wani nitsatsan wuri inda babu hayaniya, sai kayi mata sallama na tabbata zata amsamaka sannan kuma zata tsaya taji mi kakeson ka fada mata.

Saurayi….. Assalamu alaikum. Zata kalleka da gefen ido, sannan ta amsamaka. Wa alaikassalam.

Saurayi:.. Don Allah idan bazaki damuba inaso kidan bani minti biyu daga cikin lokacinki. Zatayi maka musu ta fada maka cewa Gaskiya sauri nake banason Bata lokaci. To kada kadamu,

Saurayi:… Don Allah kiyi haquri wata magana nakeson nafadamiki, zata kalleka sama da kasa ta fada ma cewa Ina sauraronk (ta daga kai sama)

Saurayi…..Haq iqa dabi’unki da riqon addininki sun dade suna birgeni, a kullum Naganki sai naji sonki yana qara mamaye zuciyata, idan bazaki damuba inaso ki bani sarari acikin zuciyarki domin na samu nakasa hajata, kuma na tabbata zanci ribar soyayya da Kauna a cikin zuciyarki. Zata danyi murmushi sannan takara kallonka sama da kasa adai dai wannan lokacinne wankanka zai danyi tasiri kadan, bayan ta gama yi maka kallo a tsanake zata mayar maka da amsa kamar haka Gaskiya ku samari ba abin yarda bane, sai mutum yabaku dama sai ku yaudareshi ku barshi acikin damuwa.

Saurayi:… Haba ya za’ayi na yaudari kyakkyawar budurwa kamarki? Ai ba duka aka taru aka zama dayaba, wallahi sonki nakeyi har zuciyata, akullum da tunaninki nake kwana nake tashi. Zatayi maka dan murmushi kadan wanda bazaisa ka rainata ba sannan ta fada maka cewa sai nayi shawara.

Saurayi:.. Shawara? To shikenan, ina sauraronki duk lokacinda kikagama shawarar amma inaso kiyimin wata alfarma guda, zata tambayeka wace irin alfarma?

Saurayi…. ina so ki sanar dani duk hukuncin da zuciyarki ta yanke, ni kuma nayi miki alkawarin cewa koda baiyimin dadi ba zuciyata da idanuwana bazasu taba ganin bakinki ba zatayi murmushi tace kada kadamu da yardar Allah zan sanar dakai.

Saurayi.… Hmmn na gode sosai. Insha Allah babu abinda zakaji sai alkhairi.

IN ALLAH YAYARDA KASACE ZUCIYAR KENAN.

Don Tambaya KO Neman Karin Bayani Yi Comment.

360hausa Team

360Hausa is a current Best Hausa Entertainment blog in Africa that specialized in providing you high quality content. 360Hausa was found and manage by Abubakar Yusuf Radda (B2 [D Promoter] Slayer). A Blogger, Ghost Writer & Content creator. Follow us on Social Media @360Hausa

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Related Articles

Back to top button