Connect with us

HAUSA NEWS

YAJIN AIKI: Ƴan Adaidaita sahu za su gane shayi ruwa ne – Baffa Babba (Shugaban Karota)

Published

on

YAJIN AIKI: Ƴan Adaidaita sahu za su gane shayi ruwa ne – Baffa Babba (Shugaban Karota)

YAJIN AIKI: Ƴan Adaidaita sahu za su gane shayi ruwa ne – Baffa Babba (Shugaban Karota)

Shugaban Karota Baffa Babba Yayi Tsokaci Kan Yajin Aikin Da Yan Adaidaita Sahu Suke Yau. Inda Ya Bayyana Ƴan Adaidaita sahu za su gane shayi ruwa ne.

Shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Ɗanagundi ya ce matuƙa baburan adaidaita sahu a Kano za su gane shayi ruwa ne.

Baffan ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ta shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio, kan yajin aikin da Ƴan Adaidaitar suka tsunduma.

Ya ci gaba da cewa, wannan yajin aiki ƙilu ce za ta jawo bau ga masu adaidaitar.

Baffan ya kuma ce, rashin fitowar su a yau, ya sanya ana bin dokokin titi a Kano.

A Litinin ɗin nan ne aka wayi gari da yajin aikin Ƴan Adaidaitar bayan da suka zargi KAROTA da cusguna musu, kan batun sabinta rajista.

Sai dai dama tun a baya KAROTA ta sha musanta hakan tana mai cewa, abin da take yi gyara kayanka ne.

FREEDOM RADIO NIG KANO.

360Hausa is a current Best Hausa Entertainment blog in Africa that specialized in providing you high quality content. 360Hausa was found and manage by Abubakar Yusuf Radda (B2 [D Promoter] Slayer). A Blogger, Ghost Writer & Content creator. Follow us on Social Media @360Hausa

Advertisement .
Click to comment

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

HAUSA NEWS

‘”Kalmar SARKI Tayi Yawa” Inji Hamisu Breaker

Published

on

'"Kalmar SARKI Tayi Yawa" Inji Hamisu Breaker

'"Kalmar SARKI Tayi Yawa" Inji Hamisu Breaker

Shahararren Mawakin Hausa “Hamisu Breaker” Yayi Godiya Ga Graphics Designer Din Da Yayi Masa Sabon “Artwork” Inda Ya Rubuta “KING” Ma’ana Sarki.

Babban Mawakin Ya Burge Mutane Inda Ya Saka Hoton A Shafin Nasa Tareda Godiya, Inda Ya Bayyana Masa “Nagode Sosai Brother Amma Kalmar Sarki Tayi Yawa”.

Isma’il Yelwa graphics Tabbas Yayi Hakan Ne Don Jinjina Ga Mawakin Ta Yanda Yake Kokari Sosai, Kuma Yayi Duba Da Yadda Mawakin Yake Haskawa A duniya.

Shima Kuma Hamisu Breaker Yayi Hakan Don Ya Nunawa Duniya Bashida Alaka Da Duk Wani Abu Da Zai Kawo Masa Tunanin Yafi Wani Balle Ya Fara Jin Girman Kai.

Shin Ya Can Canta A Fara Kiran Hamisu Breaker Sarki Kuwa ?

Continue Reading

HAUSA NEWS

Rashin ƴan Adaidaita ya sanya ana bin dokokin tuƙi – Baffa Babba Ya Bayyanawa Freedom Radio Kano

Published

on

Rashin ƴan Adaidaita ya sanya ana bin dokokin tuƙi – Baffa Babba Ya Bayyanawa Freedom Radio Kano

Rashin ƴan Adaidaita ya sanya ana bin dokokin tuƙi – Baffa Babba Ya Bayyanawa Freedom Radio Kano

Baffa Babba Ya Bayyanawa Freedom Radio Kano, Rashin ƴan Adaidaita ya sanya ana bin dokokin tuƙi.

Hukumar KAROTA a jihar Kano ta ce, rashin zirga-zirgar babura masu ƙafa a kan titinan Kano ya sanya ana yin tuƙi cikin bin doka.

Shugaban hukumar Baffa Babba Ɗan Agundi ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.

Cikin tattaunawar da aka yi da Baffa ta wayar tarho, wanda ya mayar da hankali kan batun yajin aikin da direbobin adaidaita sahu da suka tsunduma a yau.

“Za ku sha mamakin irin matakin da zai biyo baya sakamakon yajin aikin da suka shiga, domin kuwa za su gane shayi ruwa ne”.

“Mu abinda muka lura da shi ma a yau shi ne, ana gudanar da tuki cikin tsari da doka saboda rashin babura masu ƙafa uku”.

A cewar Baffa Babba Ɗan Agundi “Muna jiran umarnin gwamna ne kawai domin mu fara aiwatar da tsarin da doka ta shimfiɗa, don haka duk wanda yaga ba zai yi biyayya ba to yazo ya karɓi kuɗin sa ya ajiye baburin sa domin baya cikin halatattun masu tuƙa babur ɗin a Kano.

Sai dai daga baya Baffa Baffa ya ce, ya karɓi umarni daga wajen gwamna Gandujen kan cewa duk direban adaidaita sahun daya fita aiki a yau, aka lalata baburin sa saboda fitowa da yayi aiki ana yajin aiki da ya garzaya hukumar KAROTA domin a gyara masa.

A safiyar yau Litinin ne dai matuƙa baburan adaidaita sahu suka tsunduma yajin aiki sakamakon batun sauyin lamba da sanin ta takardun tuƙi da hukumar KAROTA ta umarce su da sauyawa.

FREEDOM RADIO KANO

Continue Reading

HAUSA NEWS

KANNYWOOD: Rarara ya baiwa Abdul D-One Da Amaryasa Kyautar Motoci Ranar Aurensu

Published

on

KANNYWOOD: Rarara ya baiwa Abdul D-One Da Amaryasa Kyautar Motoci Ranar Aurensu
KANNYWOOD: Rarara ya baiwa Abdul D-One Da Amaryasa Kyautar Motoci Ranar Aurensu

KANNYWOOD: Rarara ya baiwa Abdul D-One Da Amaryasa Kyautar Motoci Ranar Aurensu

Babban Mawakin Siyasar Arewa ” Dauda Kahutu Rarara’, Yayiwa Abdul D-One da Amaryarsa Gagarumar Kyauta Ta Motoci.

A yau ne majiyarmu ta samu labarin cewa mawaki dauda Adamu kahutu rarara ya baiwa mawaki abdul d one kyautar mota kamar yadda mai magana da yawun rarara ya fadi a shafinsa na sada zumunta

.

Chairman Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara Ya Gwangwaje Ango Abdul D. One da Amaryarsa Salma Sulaiman da Kyautar Mota Kirar Honda EOD a Ranar Auren Su, Chairman Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara Yayi Musu Fatan Allah Ya Sanya Al-Kairi Tare da Addu’ar Allah Ya Basu Zaman Lafiya.

Motoci Takwas da Babur Daya Kenan Ango da Amarya Nima Ina Tayaku Murna.

Rabi’u Garba Gaya
Media Aide to Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara APC Director General Campaign Musics.”..

Inda shima mawakin abdul d one yayi godiya ga Rarara kamar haka:.

Me Gidan Mu Kuma Dan Uwan Mu Kullum Cikin Wasa Da Dariya Muke Rabuwa Ngde Da Wannan Babbar Kyauta Kasani Farin Ciki A Ranar Farin Ciki Allah Yasaka Farin Ciki Har Abada.”

Source: Hausaloaded

Continue Reading

Trending Now

DMCA.com Protection Status