HAUSA NEWS

YAJIN AIKI: Ƴan Adaidaita sahu za su gane shayi ruwa ne – Baffa Babba (Shugaban Karota)

YAJIN AIKI: Ƴan Adaidaita sahu za su gane shayi ruwa ne – Baffa Babba (Shugaban Karota)

Shugaban Karota Baffa Babba Yayi Tsokaci Kan Yajin Aikin Da Yan Adaidaita Sahu Suke Yau. Inda Ya Bayyana Ƴan Adaidaita sahu za su gane shayi ruwa ne.

Shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Ɗanagundi ya ce matuƙa baburan adaidaita sahu a Kano za su gane shayi ruwa ne.

Baffan ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ta shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio, kan yajin aikin da Ƴan Adaidaitar suka tsunduma.

Ya ci gaba da cewa, wannan yajin aiki ƙilu ce za ta jawo bau ga masu adaidaitar.

Baffan ya kuma ce, rashin fitowar su a yau, ya sanya ana bin dokokin titi a Kano.

A Litinin ɗin nan ne aka wayi gari da yajin aikin Ƴan Adaidaitar bayan da suka zargi KAROTA da cusguna musu, kan batun sabinta rajista.

Sai dai dama tun a baya KAROTA ta sha musanta hakan tana mai cewa, abin da take yi gyara kayanka ne.

FREEDOM RADIO NIG KANO.

360hausa Team

360Hausa is a current Best Hausa Entertainment blog in Africa that specialized in providing you high quality content. 360Hausa was found and manage by Abubakar Yusuf Radda (B2 [D Promoter] Slayer). A Blogger, Ghost Writer & Content creator. Follow us on Social Media @360Hausa

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Related Articles

Back to top button