HAUSA NEWS

An Kafa Dokar Hana Tsadar Aure A Jihar Sokoto

An Kafa Dokar Hana Tsadar Aure A Jihar Sokoto

An Kafa Dokar Hana Tsadar Aure A Jihar Sokoto. Majalisar dokokin Jihar Sokoto ta sanya hannu kan wani kudirin dokar da ke sanya ido kan tsada da almubazzarancin da jama’a ke yi a bikin aure a jihar.

CHECK: Yadda Zaka Tunkari Budurwa Da Maganar Soyayya Ka Sace Zuciyarta Ta Sauki

Kudirin wanda Alhaji Abubakar Shehu na jam’iyyar APC da Faruk Balle na Jam’iyyar PDP suka gabatar, sai da aka fara gabatar da shi ga Kwamitin Kula da Al’amurran Addini a majalisar.

Shehu wanda shi ne shugaban kwamitin, ya gabatar da rahotonsu a wani zaman farko na ‘yan majalisar kuma daukacinsu suka amince ya zama doka.

Kudirin dokar na bukatar sanya ido kan almubazzarancin kudi da ake yi a yayin bikin aure da taron suna da kaciya da sauran bukukuwa a sassan jihar.

Bayan wata muhawara a zaman na farko da mataimakin shugaban majalisar ya jagoranta, Alhaji Abubakar Magaji, kudirin dokar ya samu amincewar ‘yan majalisar.

360hausa Team

360Hausa is a current Best Hausa Entertainment blog in Africa that specialized in providing you high quality content. 360Hausa was found and manage by Abubakar Yusuf Radda (B2 [D Promoter] Slayer). A Blogger, Ghost Writer & Content creator. Follow us on Social Media @360Hausa

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Related Articles

Back to top button