HAUSA NEWS

Hamisu Breaker Zai Fito A Cikin Sabon Kannywood Film Mai Suna “LULU DA ANDALU”

Hamisu Breaker Zai Fito A Cikin Sabon Kannywood Film Mai Suna "LULU DA ANDALU"

Shahararren Mawaki Hamisu Breaker Zai Fito A Cikin Sabon Kannywood Film Mai Suna “LULU DA ANDALU”.

Wannan Tabbas Babban Shiri Ne Wanda Ake Kashe Ma’Uden Kudade, Kuma Ake Warware Basira A Cikinsa.

Hamisu Breaker Best Songs Movies 2022

Babban Mawakin Na Hausa Ya Shiga Cikin Shirin Ne, a Matsayin Mawaki Wanda Aka Gayyata. Inda Ya Rera Sabuwar Wakarsa ­SO (LOVE).

Mawakin Yayi Reposting Kamar Haka:

https://www.instagram.com/tv/CbGQ4JtDYsV/?utm_medium=copy_link

Wajen dauka Shirin series film din Lulu da Andalu
Ga LULU Ga ANDALU

Bismillahir rahmanir rahim!!!

MANSA MUSA wani shaharerren mai dukiya ne daga kasar MALI wanda tarihi ya tabbatar da cewa ya taba zama mutumin da babu wanda ya kaishi dukiya a duniya, yayi mulkinsa a matsayin MANSA na MALI tsakanin shekara ta 1312 sannan ya rasu ne a shekara ta 1337.

Sai kuma kwatsam a wannan zamani namu na shekara 2022 aka sami wani bawan Allah wanda burinsa shine ya gano inda dukiyar MANSA MUSA take domin ya mallaketa, amma domin gano inda dukiyar MANSA MUSA take dole sai an taso da wasu hatsabiban Aljanu guda biyu wato LULU da ANDALU daga dogon barcinsu na shekaru sama da 700 da suka gabata.

TAMBAYA

Shin wadannan aljanu da su kadai suka san inda dukiyar nan take za’a iya taso da su kuwa?

Shin in anyi nasarar tashinsu daga dogon barcinsu zasu bayyanar da inda dukiyar MANSA MUSA take kuwa?

Shin in anyi nasarar taso da LULU da ANDALU ya rayuwa zata kasance?

Shin waye ne wannan bawan Allah da yakeson mallakar dukiyar MANSA MUSA?

Ku biyumu cikin wannan shiri Mai dogon zango da ya hada soyayya,tashin hankali, kauna, kishi, kudiri, juriya, jarumta, hatsabibanci, Amana da yaudara.

LULU DA ANDALU

Tabbas wannan series din zaizo da abubuwan gani, burgewa, nishadantarwa da darasi abin kwaikwayo.

A film by @dan_hausa1
Created and produced by @official_tyshaban
Co-Produced by: @binisah1
Gaffer by @gaffergata
Make-up @sojimakeup
DOP @jimohfilms

SHIN KUNJI DADIN KASANCEWAR HAMISU BREAKER A CIKIN WANNAN SHIRIN ?

360hausa Team

360Hausa is a current Best Hausa Entertainment blog in Africa that specialized in providing you high quality content. 360Hausa was found and manage by Abubakar Yusuf Radda (B2 [D Promoter] Slayer). A Blogger, Ghost Writer & Content creator. Follow us on Social Media @360Hausa

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Related Articles

Back to top button