HAUSA NEWS

Kotu Tayi umarni a zare ₦300,000 daga asusun kakakin ƴan sandan Kano – SP ABDULLAHI Haruna Kiyawa

Kotu Tayi umarni a zare ₦300,000 daga asusun kakakin ƴan sandan Kano - SP ABDULLAHI Haruna Kiyawa

Babbar Kotu Tayi umarni a zare ₦300,000 daga asusun kakakin ƴan sandan Kano – SP ABDULLAHI Haruna Kiyawa.

Kotun tarayya da ke Kano ta bada umarnin a cire Naira dubu ɗari uku da aka samu a asusun banki na mai magana da yawun ƴan sandan Kano SP. Abdullahi Haruna Kiyawa.

Kotun ta ce, idan aka cire kuɗin za a a biya wani matashi Bashir Bashir Galadanci da su.

A shekarar da ta gabata ne Kotun ta umarci Abdullahi Kiyawa da ya biya Galadanci diyyar naira miliyan guda sannan ya shiga kafafen yaɗa labarai ya nemi afuwarsa, saboda ɓata masa suna da yayi.

Sai dai har yanzu Kiyawan bai cika waɗannan umarni ba, abin da ya sanya Galadanci ya sake komawa Kotun inda ta umarci a bincikin asusun bankin Kiyawan, inda aka samu dubu ɗari ukun.

Freedom Radio ta so jin ta bakin SP. Kiyawa amma har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto haƙanmu bai cimma ruwa ba.

SOURCE: FREEDOM RADIO KANO

360hausa Team

360Hausa is a current Best Hausa Entertainment blog in Africa that specialized in providing you high quality content. 360Hausa was found and manage by Abubakar Yusuf Radda (B2 [D Promoter] Slayer). A Blogger, Ghost Writer & Content creator. Follow us on Social Media @360Hausa

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button