HAUSA NEWS

Baki da Ilimin Addini – Fati Slow ta shigarwa sarkin waka – Ta Ragargaje Nafisat Abdullahi

Baki da Ilimin Addini - Fati Slow ta shigarwa sarkin waka - Ta Ragargaje Nafisat Abdullahi

Baki da Ilimin Addini – Fati Slow ta shigarwa sarkin waka – Ta Ragargaje Nafisat Abdullahi.

Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman da aka fi sani da Fati Slow ta fito ta goyi bayan caccakar abokiyar sana’arsu, Nafisa Abdullahi da Naziru Ahmad ya yi kan zagin iyayen da ke tura ‘ya’yansu almajiranci. Fati Slow ta ce tabbass babu asararre sama da mutumin da zai dunga iskanci yana watsawa duniya ana zagin iyayensa amma ko a jikinsa.

Tsohuwar jarumarta bayyana cewa sai inda karfinsu wajen fada ma duk mutumin da zai zagi almajirai gaskiya. A wani bidiyo da ta saki a shafinta na Instagram inda a ciki ne ta yi shagube ga Nafisa, ta bayyana cewa jarumar bata da ilimin addini shi yasa har take iya kalubalantar tura yara almajiranci domin su koyo ilimin addininsu.

“Naziru wannan maganarka gaskiya ne babu cikakken dan iska kuma wanda iyayensa ma basu san yadda za su yi da shi ba shine wanda zai yi iskanci ya turo duniya ana ta zagin iyayenshi yana dariya, shine cikakken dan iska. “Kuma wanda yake ganin Naziru bai yi daidai ba, Naziru ya fito ya yi magana ka yi abun da za ka yi ko ki yi abun da za ki yi, ya fito nya fadi abun da ke ransa nima na fito na fadi abun da ke cikin raina.

Source: Hausa Legit NG

360hausa Team

360Hausa is a current Best Hausa Entertainment blog in Africa that specialized in providing you high quality content. 360Hausa was found and manage by Abubakar Yusuf Radda (B2 [D Promoter] Slayer). A Blogger, Ghost Writer & Content creator. Follow us on Social Media @360Hausa

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button