HAUSA NEWS

LABARI: Yadda Yan Bindiga sukayi Juyin Mulki A kauyukan Jahar Sokoto

LABARI: Yadda Yan Bindiga sukayi Juyin Mulki A kauyukan Jahar Sokoto
LABARI: Yadda Yan Bindiga sukayi Juyin Mulki A kauyukan Jahar Sokoto

Labari Da Dumi Duminsa, Yan Bindiga Sunyi Juyin Mulki, a Wasu Kauyukan Jahar Sokoto Nigeria.

Ɗan bindiga Bello Turji da yaranshi sunyi juyin mulki a wasu kauyukkan Dake karamar hukumar sabon birnin jahar Sokoto.

Yanran Bello Turji da suka hada da Ɗan Bakkwalo, Boka l Tamiske, Hassan Ɗan Kwaro, DOGO da Jammu Baki sun gayyaci mazauna kauyukkan zaman tattaunawa a kauyen Saturu ranar alhamis 04/10/2021.

Yayin Zaman ne suka umurci mazauna kauyen Gangara da su zabi daya daga cikin yan bindigar a matsayin hakiminsu Inda suka zabi dan bindiga Ɗan Bakkwalo a matsayin sabon hakinin gangara.

Nantake sabon hakimin gangara Ɗan Bakkwalo ya gindiya musu sharudda da suka hada da Bude kasuwanni da masallatai da sauransu.

A kauyen Maƙwaruwa Ɗan bidiga Boka Tamisƙe ya nada kanshin a matsayin hakiminsu Inda ya Kira Taron gaggawa da umurtar hakimin garin Mai suna Ɗan Sani da ya gayawa talakkawansa da Kansa cewa yanzu Boka Tamiske ne sabon hakiminsu ba Shiba. Via

 

360hausa Team

360Hausa is a current Best Hausa Entertainment blog in Africa that specialized in providing you high quality content. 360Hausa was found and manage by Abubakar Yusuf Radda (B2 [D Promoter] Slayer). A Blogger, Ghost Writer & Content creator. Follow us on Social Media @360Hausa

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button