HAUSA NEWS

TOFAA!!! Wata Bazawara a KANO ta fasa AURE saboda an Kawo mata kayan lefe a Cikin LEDA

TOFAA!!! Wata Bazawara a KANO ta fasa AURE saboda an Kawo mata kayan lefe a Cikin LEDA

KUNGA LAIFINTA ?… Wata Bazawara a KANO ta fasa AURE saboda an Kawo mata kayan lefe a Cikin LEDA.

Wata bazawara mai ɗa ɗaya ta fasa aurenta bayan da bazawarin da zai aure ta ya aike mata da kayan lefe a ledar bage.

Gidan rediyon Freedom ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a Jihar Kano, bayan da bazawarin, wanda a ka baiyana shi da suna Ibrahim, ya aike da kayan lefen a ledar bage, amma sai ya ga an dawo masa da kayansa.

Da ya ke shaida wa Freedom Radio, bazawarin ya ce sun ɗau lokaci su na soyayya, lamarin da har ya kai ga sun amince da su auri junansu.

Ya ƙara da cewa ganin cewa bazawara ce har da ɗa guda ɗaya, ya ce mata ba zai yi mata lefe ba da wasu gagaruman hidimomi kamar na auren fari ba, amma zai bata kuɗi ta ɗan sayi sabbin kaya, amma sai ta matsa masa cewa sai ya yi mata hidima gagaruma.

Shine shi kuma, a cewarsa, ya sai mata atamfa turmi kala 4 da takalmi, mayafi da kayan shafe-shafe da turaruka, in da ya ƙara da cewa ya kuma bata Naira dubu 30 ta sai wasu abubuwan.

“Amma bayan na kai kayan, kawai sai na ji ta kira ni ta na nuna min bacin ranta. Shine nan take ta nuna min cewa ta fasa auren. Ni kuma na ce a dawo min da kaya na da kuɗi na.

“Da a ka tashi dawo min da kayan, an dawo da su daidai amma a kuɗin an cire naira dubu 10 wai ta yi gyaran jiki da su.

“Gaskiya ban ji dadi ba amma ba komai haka Allah Ya ƙaddara,” in ji shi.

Freedom Radio ta sako muryar wata mata da ke haɗa aure, inda ta yi masa alƙawarin ya je ya zaɓi duk wacce ya ke so za a yi musu aure kafin ma watan azumin Ramadana.

– Daily Nigerian Hausa

360hausa Team

360Hausa is a current Best Hausa Entertainment blog in Africa that specialized in providing you high quality content. 360Hausa was found and manage by Abubakar Yusuf Radda (B2 [D Promoter] Slayer). A Blogger, Ghost Writer & Content creator. Follow us on Social Media @360Hausa

WHAT CAN YOU SAY ABOUT THIS ?

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Related Articles

Back to top button