Babban Shehin Darikar Tijjaniyya Ta Africa Dahiru Usman Bauchi, Yayi Sabon Furuci Akan Yan Kungiyar Izalah. Inda Ya Bayyana Abubuwa Uku, Kuma Ya Bayyana Su Akan Dalilin Da Zaisa Su Yarda su Hada Kai Da Izalah.
Wata sabuwa inji yan chacha anya wannan abubuwan da babban shehi ya kawo kungiyar izalatu bidi’ah wa’ikamatus sunnah zasuyi na’am da shi kuwa domin kuwa suna yakar bidi’a da nuna girman waliyai da Alkur’ani ya fadi da hadisan manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.
To shine a yau majiyarmu Hausaloaded munka samu rahoto daga shafin fityanulmedia sunka wallafa akan abun da shehin su yace na hadin kansu da izala.
“Idan Dan Izala Ya Daina Abubuwa Uku To Shi Kenan Zamu Hada Kai Dasu, Daman Sune Suka Tafi Suka Barmu Suka Ce Mu Ba Musulmai Bane, Suke Kafirta Musulmi Amma Mu(Dariqa) Bamu Da Abokin Gaba Kullum Kofarmu a Bude Take Don Hadin Kai Idan Har Suka Dawo Suka Daina Yin Wadannan Miyagun Laifukan:
*1. Kafirta Musulmi.
*2. Kafirta Dariku.
*3. Sannan Suka Daina Kafirta Waliyyai.
Shi Kenan Hadin Kai Ya Zo Amma Muddin Basu Daina Ba, Muna Nan Kamar Kullum Bamu Canja Ba”.
….Inji SHAYKH TAHIRU USMAN BAUCHI.” Via.